John 20

Kabarin da Ba Kowa

1Da sassafe a ranar farko ta mako, tun da sauran duhu, Maryamu Magdalin ta tafi kabarin ta kuwa tarar an kawar da dutsen daga bakin kabarin. 2Sai ta zo da gudu wajen Siman Bitrus da ɗayan almajirin, wanda Yesu yake ƙauna, ta ce, “Sun ɗauke Ubangiji daga kabarin, ba mu kuma san inda suka sa shi ba!”

3Sai Bitrus da almajirin nan suka nufi kabarin. 4Dukansu biyu suna gudu, amma ɗayan almajirin ya tsere wa Bitrus ya kuma fara kai kabarin. 5Ya sunkuya ya duba ciki ya ga ƙyallayen lilin ne kwance a can amma bai shiga ba. 6Saʼan nan Siman Bitrus, wanda yake bayansa, ya iso ya kuwa wuce cikin kabarin. Ya ga ƙyallayen lilin kwance a can, 7haka ma zanen binnewar da aka naɗe kan Yesu da shi. Zanen a naɗe yake shi kaɗai, a keɓe da lilin ɗin. 8A ƙarshe sai almajirin nan, wanda ya kai kabarin da farko, shi ma ya shiga. Ya gani ya kuma gaskata. 9(Har yanzu ba su fahimci Nassin nan da ya ce lalle ne Yesu yǎ tashi daga matattu ba.)

Yesu Ya Bayyana ga Maryamu Magdalin

10Sai almajiran suka koma gidajensu, 11amma Maryamu ta tsaya a bakin kabarin daga waje tana kuka. Da tana cikin kuka, sai ta sunkuya ta leƙa cikin kabarin, 12sai ta ga waɗansu malaʼiku biyu saye da fararen tufafi, zaune a inda dā gawar Yesu take, ɗaya wajen kai ɗayan kuma wajen ƙafafu.

13Suka tambaye ta cewa, “Mace, don me kike kuka?”

Ta ce, “Sun ɗauke Ubangijina, ban kuma san inda suka ajiye shi ba.”
14Da ta faɗin haka, sai ta juya ta ga Yesu tsaye, sai dai ba ta gane cewa Yesu ne ba.

15Sai ya ce, “Mace, don me kike kuka? Wa kike nema?”

Ta yi tsammani shi ne mai aikin lambun, sai ta ce, “Ranka yǎ daɗe, in kai ne ka ɗauke shi, gaya mini inda ka ajiye shi, in je in ɗauke shi.”

16Yesu ya ce mata, “Maryamu.”

Sai ta juya wajensa ta ɗaga murya ta ce da Aramayanci, “Rabboni” (wanda yake nufin Malam).

17Yesu ya ce, “Kada ki riƙe ni, gama ban riga na koma wajen Uba tukuna ba. A maimako, ki tafi wajen ʼyanʼuwana ki gaya musu, ‘Ina komawa wajen Ubana da Ubanku, wajen Allahna da kuma Allahnku.’ ”

18Sai Maryamu Magdalin ta wajen almajiran da labari cewa: “Na ga Ubangiji!” Ta kuma gaya musu cewa ya faɗa mata waɗannan abubuwa.

Yesu Ya Bayyana ga Almajiransa

19Da Yamman ranar farko ta mako, saʼad da almajiran suna tare, ƙofofi kuma suna a kulle saboda tsoron Yahudawa, sai ga Yesu ya zo ya tsaya a tsakiyarsu ya ce, “Salama ta kasance tare da ku!” 20Bayan ya faɗa haka, sai ya nuna musu hannuwansa da gefensa. Sai almajiran suka yi farin ciki ƙwarai da suka ga Ubangiji.

21Sai Yesu ya sāke ce musu, “Salama ta kasance tare da ku! Kamar yadda Uba ya aiko ni, haka ni ma ina aikan ku.” 22Da wannan sai ya hura musu numfashinsa ya ce, “Ku karɓi Ruhu Mai Tsarki. 23Duk wanda kuka gafarta wa zunubansa, an gafarta masa ke nan. Duk wanda ba ku gafarta wa ba kuwa, ba a gafarta masa ba ke nan.”

Yesu Ya Bayyana ga Toma

24Toma kuwa, (wanda ake kira Didaimus), ɗaya daga cikin Sha Biyun, ba ya tare da almajiran saʼad da Yesu ya zo. 25Saboda haka sauran almajiran suka ce masa, “Ai, mun ga Ubangiji!”

Amma ya ce musu, “Ina, ai, sai na ga ramin ƙusa a hannuwansa na sa yatsata a inda ƙusoshi suka kasance, na kuma sa hannuna a gefensa, in ba haka ba ba zan gaskata ba.”

26Bayan mako guda, har wa yau almajiransa suna cikin gidan, Toma kuwa yana tare da su. Ko da yake ƙofofi suna kulle, sai ga Yesu ya zo ya tsaya a tsakiyarsu ya ce, “Salama ta kasance tare da ku!” 27Saʼan nan ya ce wa Toma, “Sa yatsarka nan; dubi hannuwana. Miƙa hannunka ka sa a gefena. Ka daina shakka ka gaskata.”

28Toma ya ce masa, “Ya Ubangijina da Allahna!”

29Sai Yesu ya ce masa, “Wato, ka gaskata saboda ka gan ni ne, masu albarka ne waɗanda ba su gan ni ba, amma suka gaskata.”

30Yesu ya yi waɗansu abubuwan banmamaki da yawa a gaban almajiransa da ba a rubuta a wannan littafi ba. 31An dai rubuta waɗannan ne don ku gaskata Yesu ne Kiristi, Ɗan Allah kuma ta wurin gaskatawa ku sami rai a cikin sunansa.

Copyright information for HauSRK